'Yan uwan Kanar Abu Ali sun zargi sojin Nigeria

'Yan uwan Kanar Abu Ali sun zargi sojin Nigeria - Hello people APPSGAMEZONE, In the article you are reading right now with the title 'Yan uwan Kanar Abu Ali sun zargi sojin Nigeria, We have prepared this article for you to read and retrieve information therein. Hopefully the contents of this post Article news, Article Nigerian, We write this you can understand. well, happy reading.

Judul : 'Yan uwan Kanar Abu Ali sun zargi sojin Nigeria
link : 'Yan uwan Kanar Abu Ali sun zargi sojin Nigeria

Baca juga


'Yan uwan Kanar Abu Ali sun zargi sojin Nigeria

'Yan uwan marigayi Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, kwamandan rundunar sojin kasar ta 272 mai kula da tankokin yaki, da 'yan Boko Haram suka kashe a jihar Bornon Najeriya sun zargi rundunar sojin kasar da rashin ba shi hutu.



Amina Abu Ali, kanwar Muhammad Abu Ali, ce ta yi wannan koke lokacin da wata kungiya mai rajin kare hakkokin sojin Najeriya da suka rasa rayukansu a lokutan yaki ta je yi musu ta'aziyya a Kaduna.

A cewarta, "Muna fatan sojin Najeriya za ta kammala yaki da 'yan Boko Haram domin gudun ci gaba da asarar zaratan sojin kasar".

Ta kara da cewa ya kamata a canza lokacin da sojoji ke shafewa a fagen daga domin "idan sun dade a can akwai gajiya.

Sojoji na nan ko'ina, ba wai wasu sojoji ne kawai za su yi wannan yakin ba".
Ta ce
"Dan uwana ya zauna a Maiduguri tsawon shekara biyu, amma hutun mako biyu kawai aka ba shi."

Manema Labarai Sun tuntubi Kakakin rundunar sojin kasa kan wannan zargi, amma har yanzu ba mu samu amsa ba.

A ranar Litinin din da ta gabata ne aka yi jana'izar Muhammad Abu Ali tare da wasu sojoji hudu.

Sun mutu ne lokacin da suke kokarin dakile wani harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a barikin sojin kasar na 119 da ke garin Malam Fatori a jihar Borno.

Kafin rasuwarsa, Kanar Ali ya taka rawa sosai wurin kwato wasu garuruwa daga hannun Boko Haram, abin da ya sa aka yi masa karin girma.

Baya ga iyalan Kanar Ali, sojoji da dama da ke fafatawa a yankin Arewa maso Gabas, na kokawa kan rashin musanya su da karancin samun hutu.


This is the end of my post today. 'Yan uwan Kanar Abu Ali sun zargi sojin Nigeria

I hope we can take a good lesson from 'Yan uwan Kanar Abu Ali sun zargi sojin Nigeria what I post today. I ask forgiveness for any words and behave which are not supposed to be. Thank you for your kind attention today. Hopefully can give benefits to all of you. well, see you in other articles.

You are now reading the article 'Yan uwan Kanar Abu Ali sun zargi sojin Nigeria with the link address https://appsgamezone.blogspot.com/2016/11/uwan-kanar-abu-ali-sun-zargi-sojin.html

0 Response to "'Yan uwan Kanar Abu Ali sun zargi sojin Nigeria"

Post a Comment