Labarai: "Yan PDP sunce Zasu ceto kasar nan daga hannun yan APC"

Labarai: "Yan PDP sunce Zasu ceto kasar nan daga hannun yan APC" - Hello people APPSGAMEZONE, In the article you are reading right now with the title Labarai: "Yan PDP sunce Zasu ceto kasar nan daga hannun yan APC", We have prepared this article for you to read and retrieve information therein. Hopefully the contents of this post Article news, Article Nigerian, We write this you can understand. well, happy reading.

Judul : Labarai: "Yan PDP sunce Zasu ceto kasar nan daga hannun yan APC"
link : Labarai: "Yan PDP sunce Zasu ceto kasar nan daga hannun yan APC"

Baca juga


Labarai: "Yan PDP sunce Zasu ceto kasar nan daga hannun yan APC"

– Jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Sanata Ahmed Makarfi ta kafa kwamiti mai dauke da membobi 115 a shirin da take na ganin ta karbi mulki a zaben 2019

– Jigon jam’iyyar PDP a jihar Neja, Farfesa Jerry Gana shi yake jagorantar kwamitin



A yayin kaddamar da kwamitin a Abuja ranar Talatar da gabata, Makarfi ya bayyana cewa kwamitin zai kuma bada shawarwari kan yadda jam’iyyar za ta dawo da karfinta.

Ya ce ba wai an kafa kwamitin bane saboda rikicin jam’iyyar, a’a an kafa shine domin ci gaban siyasa da kuma ceto kasar.

A wani labarin kuma dai a farkon makon nan ne dai Shugabannin jam’iyyar PDP na arewa maso gabas sun yi taronsu a Bauchi inda suka amince cewar rikicin jam’iyyar ya samo asali ne daga yankinsu tun daga lokacin da Bamanga Tukur ya rike shugabancin jam’iyyar har ya kawo kan Modu Sheriff.

Yayinda aka ba Modu Sheriff shugabancin jam’iyyar watanni ukku ya kamata yayi domin ya kammala wa’adin yankin arewa maso gabas kana ya shirya zaben da zai fitar da shugaba amma bai yi hakan ba.
Idan har jam’iyyar ta kasa warware rikicin da ta fada ciki yanzu ta hanyar lumana wasu na ganin wani bangare na iya hada kai da wasu jam’iyyun domin kafa wata daban.

Alhaji Adamu Maina Waziri wani jigon jama’iyyar kuma tsohon ministan harkokin ‘yansanda a zamanin mulkin Obasanjo yace a matsayinsu na mutanen yankin arewa maso gbas inda Ali Modu Sheriff ya fito suna kira gareshi ya daina abun da ya keyi. Yace ya isa haka nan. Tunda wa’adinshi ya kare ya sauka. Yace taronsu shi ne zai nuna masa cewa a gida ma sun kalubalanceshi bisa abun da ya keyi.

Bisa tsarin jam’iyyarsu Alhaji Waziri yace uwar jam’iyya ta ba Ahmadu Makarfi izinin ya yi shugabanci na wucin gadi kana ya shirya taron da zai fitar da sabbin shugabanni saboda haka Modu Sheriff dole ne ya kau.

Sanata Abdul Ningi daya daga cikin mamban kwamitin riko da jam’iyyar ta kafa yace tabbas rikicin PDP ya samo asali ne daga shiyar arewa maso gabas, wato yakinsu. Yace yankinsu aka ba shugabanci na shekara hudu. Saura watanni ukku su kammala aka dauko Modu Sheriff ya cika watanni ukkun domin a yi zabe.

Hajiya Zainab Maina tsohuwar minista kuma shugabar mata kuma ‘yar kwamitin amintattun jam’iyyar tace sun zo taron tattaunawa ne domin su gayawa kansu gaskiya kan dalilan da suka sa jam’iyyar ta fadi zaben 2015.

Shi ma Alhaji Shehu Musa Gaban daya daga cikin wadanda suka kafa PDP tun farkonta yace makasudin taron shi ne fito da hanyar da zasu gyara jam’iyyar.


This is the end of my post today. Labarai: "Yan PDP sunce Zasu ceto kasar nan daga hannun yan APC"

I hope we can take a good lesson from Labarai: "Yan PDP sunce Zasu ceto kasar nan daga hannun yan APC" what I post today. I ask forgiveness for any words and behave which are not supposed to be. Thank you for your kind attention today. Hopefully can give benefits to all of you. well, see you in other articles.

You are now reading the article Labarai: "Yan PDP sunce Zasu ceto kasar nan daga hannun yan APC" with the link address https://appsgamezone.blogspot.com/2016/11/labarai-pdp-sunce-zasu-ceto-kasar-nan.html

0 Response to "Labarai: "Yan PDP sunce Zasu ceto kasar nan daga hannun yan APC""

Post a Comment